Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun
kama wani mutum da ya shahara wajen hada
bama–bamai ga mayakan kungiyar Boko Haram.
Rundunar ta ce an kama Adamu Hassan ne da
ake yi wa lakabi da suna ‘Baale’ a garin Kaltungo
na jihar Gombe da ke shiyyar arewa maso
gabashin kasar.
Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya
Dole Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce an kama
mutumin ne a wani samame da jami’an hukumar
tsaro ta farin kaya suka kai.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ambato
Kanar Nwachukwu na cewa dakarun sojin kasar
sun kashe mayakan Boko Haram uku a bata
kashi da suka yi a tsaunukan Bokko Hilde da ke
kan hanyar Ngoshe zuwa Pulka a jihar Borno.