Kaftin din Barcelona, Andres Iniesta, ya ce zai
bar kungiyar da ke kasar Spain a karshen
wannan kakar.
Dan wasan na tsakiya, mai shekara 33, ya buga
wasanni 669, inda ya ci kofi 31 a Barcelona.
Iniesta kuma ya ci wa Spain kofin duniya da
kofin Turai guda biyu.
Ya kasance muhimmin dan wasa a Barcelona,
inda a nan ne ya fara taka leda tun kuriciyarsa.
A lokacin da yake bayar da sanarwar cewa zai
bar kungiyar, Iniesta ya ce “wannan wata rana
ce mai wahala a gare ni”
Iniesta, ya buga wa Spain wasanni 125, kuma
yana cikin ‘yan wasan kasar da za su buga gasar
cin kofin duniya a Rasha a bana.
Ya ci gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 da
gasar cin kofin kasashen Turai a 2008 da kuma
2012 – baya ga gasar zakarun Turai hudu da
kuma gasar La Liga takwas da ya lashe – tare da
wasu kofuna da dama da ya ci wa Barcelona.
669
Wasan da ya buga wa Barcelona
125
Wasan da ya buga wa Spain
Nasarorin Iniesta
A Barcelona da Spain
31 Yawan kofin da ya lashe a Barca
3 Kofin da ya ci wa Spain
456 Wasannin da ya yi nasara a Barcelona
85 Wasannin da ya yi rashin nasara a
Barcelona. Ya yi canjaras 128