Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a
gaban kotu inda ta ke tuhumar jagoran kungiyar
‘Yan Uwa Musulmi ta ‘Yan Shi’a Sheik Ibrahim
El-Zakzaky da kisan wani soji.
Kisan sojan na cikin tuhumce-tuhumce takwas
da gwamnatin ta shigar a gaban kotun a kan
malamin da wasu karin mutum uku.
Sauran mutanen biyu da ake zarginsu tare sun
hada da Yakub Katsina da Sanusi Koki –
shugabannin kungiyar a jihohin Katsina da Kano.
Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke
tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai
lokacin da suka yi arrangama da ‘yan shia a
garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na
shekarar 2015.
Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran ‘yan
Shi’a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe
mutum sama da 300.
Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen
da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan an yi
awangaba da wasu da dama.
Tun daga lokacin ne hukumomi ke tsare da
Sheikh Zakzaky da matarsa Zinatu a wani wuri
da ba a bayyana ba, duk da cewa kotu ta bayar
da izinin a sake su a lokuta daban daban.
Gwamnati jihar Kaduna ta kuma bayyana
kungiyar a matsayin haramtaciyya kuma ta
hanata yin taro a cikin jihar.
A farkon watan da mu ke ciki magoya bayan
Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin
lumana a kowace rana inda suka nemi a sako
mu su jagoran nasu.
Ibrahim El-zakzaky ya yi shekara biyu yana tsare
ba tare an gurfanar da shi a gaban kotu ba, in
ban da yanzu da gwamnatin jihar Kaduna ta
shigar da kara a gaban kotu.
Gwamnatin Najeriya ta ce tana tsare da jagoran
‘yan na Shi’a da kuma matarsa soboda tsaron
lafiyarsu.
A baya ta gabatar da su a gaban ‘yan jarida inda
malamin ya ce yana cikin koshin lafiya.
Ko da yake daga bisani lauyansa Femi Falana ya
ce an shirya taron manema labaran ne ba tare da
sanin jagoran ‘yan Shi’ar ba.
Rahotanni sun ce idan aka samesu da laifi za a
iya yanke mu su hukuncin kisa.