BestArewaMusic

Contact us For Music/Video Promotion Whatsapp: 09074457714, 07043434153 Email :bestarewamusic@gmail.com

Trending

Search BestArewaMusic

Sunday, 1 April 2018

Kun ga sunayen 'yan PDP da 'suka saci' kudin Najeriya?
Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen
jami'an jam'iyyar PDP mai hamayya wadanda
take zargi da satar kudin kasar.

Sai dai PDP ta ce babu daya daga cikin dukkan
mutanen da aka fitar da sunayensu da kotu ta
samu da laifi.

Ministan watsa labaran kasar Lai Mohammed ne
ya fitar da sunayen wadanda ta ce "somin tabi
ne" bayan PDP ta kalubalanci gwamnatin
Shugaba Muhammadu Buhari ta fadi 'yan PDPn
da suka saci kudin kasar.

A cewar Lai Mohammed, 'yan PDPn sun hada da
shugabanta na yanzu Uche Secondus, ranar 19
ga watan Fabrairun 2015, ya karbi N200m daga
ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan
sha'anin tsaro.

Kazalika sakataren kudi - ranar 24 ga watan
Oktoban 2014, ya karbi N600m daga ofishin mai
bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin
tsaro.

Sauran 'yan PDPn da gwamnatin Shugaba Buhari
ta zarga da satar kudin kasar su ne: kakakin
jam'iyyar na wancan lokacin Olisah Metuh, wanda
yake fuskantar tuhuma kan karbar N1.4bn daga
ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan
sha'anin tsaro.

Haka kuma, ana zargin wani jigo a jam'iyyar, mai
gidan talabijin na AIT Dr. Raymond Dokpesi,
wanda ke gaban kotu bisa zargin karbar N2.1bn
shi ma daga ofishin mai bai wa shugaban kasa
shawara kan sha'anin tsaro.

Alhaji Lai Mohammed ya ce mai bai wa tsohon
shugaban kasa Good luck Jonathan shawara,
Dudafa Waripamo-Owei, na cikin barayin da suka
saci kudin kasar inda aka gano ya ajiye N830n a
asusu hudu, yayin da ake zargi wani dan uwan
tsohon shugaban Robert Azibaola, da karbar
$40m daga ofishin mai bai wa shugaban kasa
shawara kan sha'anin tsaro.

Ministan watsa labaran ya ce "wadannan sunaye
da muka fitar somin tabi ne kuma ba mu ne
muka kirkiro labarin satar da suka yi ba. Akasarin
wadannan mutane na gaban kotu; wasu daga
cikinsu ma suna so kotu ta yarda su ba da wani
kaso na kudin domin ta sake su."

Sai dai PDP ta ce an wallafa sunayen 'ya'yanta
ne kawai da zummar bata musu suna, tana mai
cewa "babu daya daga cikin mutanen da aka
wallafa sunansa da kotu ko wata hukumar bincke
mai zaman kansa suka samu da laifi."

Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter
ta ce, "jerin sunayen da ministan watsa labarai
Alhaji Lai Mohammed ya wallafa na nuna cewa
APC da shugaban Najeriya ba su da wata hujja
da ke nuna PDP na da laifi."

Masana harkokin siyasa na ganin irin wannan
jayayya da ke faruwa tsakanin APC da PDP za ta
hana aiwatar da ayyukan ci gaban kasar, inda za
a mayar da hankali kan harkokin siyasa.


No comments:

Post a comment