• About
  • Contact Us
  • DMCA/Disclaimer
  • Privacy Policy
  • Sample Page
BestArewaMusic
No Result
View All Result
No Result
View All Result
BestArewaMusic
No Result
View All Result
  • Music
  • Videos
  • Hausa HipHop Music
  • News
  • International NEWS
  • Sports
Home News

Kwankwaso ko Atiku: Wa zai ja da Buhari a 2019?

AB Gentle by AB Gentle
April 9, 2018
in News
Reading Time: 12 mins read
0
42
SHARES
220
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter


Kodayake Shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta sake
tsayawa takara a zaben 2019 ba, amma na kusa
da shi sun sha bayyana cewa babu abin da zai
hana shi yin tazarce.

A watan Mayun shekarar 2015 ne Shugaba
Buhari ya yi rantsuwar fara mulkin wa’adin
shekara hudu karkashin jam’iyyar APC, kuma
yana da damar sake neman wa’adi na biyu a
zaben shekarar 2019.

Sai dai akwai wadanda suke ganin bai kamata
shugaban ya nemi tazarce ba, ciki har da tsohon
Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Mun yi nazari kan mutanen da ake ganin za su
iya kawar da Shugaba Muhammadu Buhari daga
kan mulki a zabe mai zuwa?
Sanata Bukola Saraki
Mutum na biyu cikin manyan ‘yan siyasar kasar
wanda ake ganin watakila ya nemi tsayawa
takarar shugabancin Najeriya shi ne Shugaban
Majalisar Wakilai Sanata Bukola Saraki.

Kodayake a halin yanzu ya musanta hakan,
amma a baya sau biyu yana neman tsayawa
takarar shugabancin kasar.
Sai dai wadansu suna ganin da wuya Sanata
Saraki ya iya samun tikitin takarar shugabancin
kasa a jam’iyyarsa ta APC, musamman ma idan
Shugaba Buhari zai yi takara.

Amma dai yana da alaka da ‘yan siyasa, ga kudi,
ga kuma kwarewa a siyasance.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Har ila yau, a zauren majalisar dattawan kasar,
akwai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi
ma ya taba neman shugabancin kasar a 2015
amma Buhari ya kayar da shi a zaben cikin gida
a APC.

Kodayake a wannan karon bai bayyana aniyyarsa
ba tukunna, amma alamu na nuna cewa har
yanzu bai hakura ba, kuma watakila ya kara
gwada sa’arsa.

Tsohon gwamnan jihar Kanon shi ne ya zo na
biyu a zaben fidda gwani na ‘yan takarara neman
shugabancin a jam’iyyar APC a zaben 2015.

Masana suna ganin a wannan karon, zai iya
samun tikitin shugabancin kasa a jam’iyyar
musamman idan Shugaba Buhari ya ki amincewa
ya sake yin takara.

Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji
Atiku Abubakar yana daya daga cikin mutanen da
ake ganin za su sake gwada sa’arsu, bayan ya
nemi zama shugaban kasar har sau uku a baya.
Akwai wadanda suke ganin sha’awarsa ta zama
shugaban Najeriya ce ta sa ya koma jam’iyyar
PDP daga jam’iyyar APC mai mulki a watan
Disambar bara.

Ga dukkan alamu Alhaji Atiku Abubakar yana
ganin zai fi samu damar kara gwada sa’arsa a
jam’iyyar PDP.

Sai dai wasu na ganin ba lallai ne jam’iyyar ta ba
shi tikitinta ba.

Ayodele Fayose

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose shi ne
wanda ya fara bayyana aniyyarsa ta tsayawa
takarar shugabancin Najeriya a karkashin
jam’iyyar PDP.

Gwamnan Fayose wanda an riga an fara yada
hotunan kamfe dinsa a fadin kasar, mutum ne da
ke yawan nuna adawarsa ga jam’iyyar APC da
kuma Shugaba Buhari.

Gwamnoni suna da matukar tasiri a siyasar
Najeriya, abin da ya sa wadansu masana suke
ganin kila shi ya sa Mista Fayose yake kokarin
ganin ya gwada sa’arsa.

Alhaji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa yana daya daga
cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya da ake ganin
watakila shi ma ya nemi takarar shugabancin
kasar a zaben 2019.

Sai dai shi ma bai fito fili ya bayyana aniyyarsa
ta yin hakan ba tukunna.

Alhaji Sule Lamido yana daya daga cikin
wadanda suke sukar gwamnatin APC da Shugaba
Buhari.

Malam Jafar Jafar wani mai sharhi ne kan
harkokin siyasar Najeriya, kuma ya ce yana ganin
duk wani dan siyasa da yake neman takara a
jam’iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne
kawai, “matukar Shugaba Buhari zai sake yin
takara.”
Ya ce: “Idan har Buhari zai yi takara, to babu
makawa jam’iyyarsa shi za ta tsayar a zaben
2019.”

“Kuma da wahala a ce ba zai yi takara ba,” in ji
shi.

Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu
muradin yin takara a jam’iyyar APC shi ne kawai
su sauya jam’iyya.

“Ga jam’iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi
murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar
jam’iyyar APC za ta iya faduwa zabe.”
“Saboda a gaskiya farin jinin jam’iyyar da na
Shugaba Buhari ya ragu sosai.”

Mai fashin bakin ya ce abin da ya sa manyan
‘yan siyasar kasar ba su fito sun bayyana
aniyarsu ta takara ba, “shi ne kamar wata dabara
ce suke don su fito tashi guda idan lokacin fara
yakin neman zabe ya yi.”

‘Yan kasar dai sun zuba ido su ga jerin mutanen
da za su fito su bayyana aniyarsu ta neman
kuri’unsu.

Previous Post

Najeriya: Buhari zai fara ziyarar aiki a Burtaniya

Next Post

(MUSIC): Legendary Mixer Ft. Jesse Jagz & BOC Madaki – Do

AB Gentle

AB Gentle

I Take Pictures Drink Chapman Eat And Sleep, CA Pro Graphics Designer, Cinematographer and A Blogger by Profession

Related Posts

Shehi Tajul'izzi - Ayi Hakuri

Shehi Tajul’izzi – Ayi Hakuri

by AB Gentle
March 24, 2023
0

...

U.S Department of State Tunisia Undergraduate Scholarship Program 2023 (Fully funded)

U.S Department of State Tunisia Undergraduate Scholarship Program 2023 (Fully funded)

by AB Gentle
March 24, 2023
0

...

Scholarship Search Tips and Secrets Every Student Should Know

Scholarship Search Tips and Secrets Every Student Should Know

by AB Gentle
March 24, 2023
0

...

NDLEA Recruitment Exercise for Young Nigerian Graduates 2023

NDLEA Recruitment Exercise for Young Nigerian Graduates 2023

by AB Gentle
March 24, 2023
0

...

Applications Open for 2023 Hammarskjöld Journalism Fellowships

Applications Open for 2023 Hammarskjöld Journalism Fellowships

by AB Gentle
March 24, 2023
0

...

Next Post

(MUSIC): Legendary Mixer Ft. Jesse Jagz & BOC Madaki - Do

Mutum 257 sun mutu' a hatsarin jirgi a Aljeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SEARCH BAM

No Result
View All Result

ADVERTISMENT

HOT ENTRIES

Shehi Tajul'izzi - Ayi Hakuri

Shehi Tajul’izzi – Ayi Hakuri

March 24, 2023
U.S Department of State Tunisia Undergraduate Scholarship Program 2023 (Fully funded)

U.S Department of State Tunisia Undergraduate Scholarship Program 2023 (Fully funded)

March 24, 2023
Scholarship Search Tips and Secrets Every Student Should Know

Scholarship Search Tips and Secrets Every Student Should Know

March 24, 2023
NDLEA Recruitment Exercise for Young Nigerian Graduates 2023

NDLEA Recruitment Exercise for Young Nigerian Graduates 2023

March 24, 2023
Applications Open for 2023 Hammarskjöld Journalism Fellowships

Applications Open for 2023 Hammarskjöld Journalism Fellowships

March 24, 2023
  • About
  • Contact Us
  • Privacy Policy
  • DMCA/Disclaimer

Copyright © 2016 - 2023 BestArewaMusic Inc.

No Result
View All Result
  • Music
  • Videos
  • Hausa HipHop Music
  • News
  • International NEWS
  • Sports

Copyright © 2016 - 2023 BestArewaMusic Inc.