Mutum 257sun mutu a hatsarin jirgin soji da ya
faru a arewacin Aljeriya, a cewar ma’aikatar
tsaron kasar.
Lamarin ya faru ne da jim kadan bayan tashin
jirgin daga filin jirgin sama na sojoji da ke
Boufarik ksa da Algiers babban birnin kasar. da
safiyar Laraba.
Akasarin wadanda suke cikin jirgin sojoji ne da
kuma iyalansu ,a cewar ma’aikatar tsaro.
Akawai ma’aikatan jirgi sama 10 da suka mutu a
cikin hatsarin jirgin.
Kawo yanzu ba bu cikakken bayani akan abinda
ya janyo hatsarin jirgin sama .
Kafar talbijin ta kasar ta ce, motocin daukar
marasa lafiya 14 sun isa wajen da lamarin ya
afku inda aka dauki wadanda suka jikkata zuwa
asibiti.
Wannan lamari dai ya faru ne a safiyar ranar
Laraba a filin jirgin saman soji na Boufarik da ke
kusa da babban birnin kasar Algiers.
Hotunan wajen da lamarin da ya afku sun nuna
yadda hayaki ke fitowa daga tarkacen jirgin a
filin.
Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron kasar ta
ce, shugaban rundunar sojin kasar, ya bayar da
umarnin a gudanar da bincike a kan musabbabin
afkuwar hadarin, inda kuma zai kai ziyara wajen.
Karin bayani
Kafar yada labarai ta Algerie24, ta ruwaito cewa,
fiye da sojoji 200 ne a cikin jirgin.
Yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya
ce mutane da dama sun mutu a cikin jirgin.
Shekara hudu da suka gabata wani jirgi da ya
dauki sojoji da iyalansu ya yi hadari a kasar ta
Algeria, inda mutum 77 suka rasa rayukansu.
Ana dai yawan samun hadarin jirgin sama a
kasashe da dama inda ake kuma asarar rayuka.
Ko a watan Fabrairun 2018 ma, wani jirgin sama
ya fadi a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a
lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa
daga Tehran zuwa Yasuj da ke kudu maso
yammacin Iran inda mutum 66 suka mutu.