A Najeriya, wasu mukarraban shugaban kasar
sun ce an yi mummunar fahimta game da
kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi
cewa mafi yawan matasan kasar cima zaune ne.
Shugaba Buhari yana magana ne a taron
kasashen renon Ingila dake gudana a birnin
Landan.
Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a
tsakanin matasan kasar musamman a kafafen
sada zumunta na zamani.
Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan
kalaman da suka ce na zubar da kima ne.
Sai dai mai bai wa shugaban shawara kan
kafafen watsa labarai Sha’aban Sharada ya ce
matasa ba su fahimci kalaman shugaba Buhari
ba.
Ya ce “duk wanda ya kalli bidiyon Shugaba
Muhammadu Buhari zai ga cewa ya furta
kalaman ne cikin raha”.
Sha’aban Sharada wanda ke cikin ‘yan tawagar
shugaban kasar dake ziyara a Landan ya ce
furucin da Shugaba Buhari ya yi hannunka mai
sanda ne ga al’ummar kasar domin su tashi
tsaye wajen neman na kansu.
Ya ce a kowane lokaci batun yadda za’a inganta
rayuwar matasa shi ne babban abunda Shugaba
Buhari ya sa a gaba.