BestArewaMusic | Northern Most Visited Entertainment Platform

Contact us For Music/Video Promotion Whatsapp: 09074457714, 07043434153 Email :bestarewamusic@gmail.com

Trending

Search BestArewaMusic

Monday, 9 April 2018

Najeriya: Buhari zai fara ziyarar aiki a Burtaniya


Shugaba Muhammadui Buhari zai fara wata
ziyarar aiki a Burtaniya, inda ake sa ran zai
gana da firayi ministar Burtaniya da shugannnin
wasu kamfanonin hakar mai.

Ana sa ran shugaban ya bar Abuja zuwa birnin
Landan a ranar Litinin.

Sanarwar ta kuma ce shugaba Buhari zai
tattauna da Archbishop na Canterbury Justin
Welby, wanda abokinsa nedomin inganta
zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-
daban na cikin kasar da ma duniya.
Shugaba Buhari zai kuma gana da wasu manyan
jami'ai daga Burtaniya da 'yan Najeriya masu
zama a kasar.

Bayan ganawa da Misis Theresa May, ana sa ran
shugaban zai halarci taron shugabannin
kasashen kungiyar rainon Ingila - Commonwealth
daga 18 ga watan Afrilu 2018.

Shugaba Buhari zai kuma gana da shugaban
kamfanin mai na Royal Dutch Plc, Mista Ben van
Beurden, da na kamfanin mai na Shell dangane
da batun zuba jari na dala biliyan 15 a tattalin
arzikin Najeriya.

Bayanan na cikin wata sanarwa da kakakin
shugaban Garba Shehu ya raba wa kafofin watsa
labarai.

Sanarwar ta ce shugaban na Najeriya na kallon
ganawar a matsayin wata damar tallafa wa
tattalin arzikin Najeriya na shekara 20 masu
zuwa.

Sanarwar ta kuma ce shugaba Buhari zai
tattauna da Archbishop na Canterbury Justin
Welby, wanda abokinsa nedomin inganta
zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-
daban na cikin kasar da ma duniya.

Shugaba Buhari zai kuma gana da wasu manyan
jami'ai daga Burtaniya da 'yan Najeriya masu
zama a kasar.


No comments:

Post a comment