A ranar Talata ne Juventus za ta karbi bakuncin
Real Madrid a wasan gab da na kusa da na
karshe a gasar Zakarun Turai.
A bara dai Madrid ce ta kungiyar a wasan
karshe na gasar, abin da ya ba ta damar daukar
kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya.
A koawace karawa da Madrid ta taba yi da
Juventus, Ronaldo yana samun zura kwallo a
raga.
Sau 19 kungiyoyin suna haduwa a tarihin gasar
Zakarun Turai -Madrid ta yi nasara a wasanni
tara, yayin da Juventus ta samu nasara a
wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a
wasanni biyu.
Hakazalika, duka kungiyoyin biyu kowace ta zura
wa abokiyar karawarta kwallaye 22 ne a raga a
tarihin karawarsu.