Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sake kwato
mutum fiye da 1,000 daga hannun mayakan
Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Ta kara da cewa yawancin mutanen da aka
kwato mata ne da yara da kuma samari da aka
tilastwa zamowa mayakan kungiyar.
A jerin sakonnin da ta wallafa a shafinta na
Twitter, rundunar sojin ta ce an ceto mutanen ne,
wadanda suka fito ne daga kauyukan Karamar
Hukumar Bama a jihar Borno, da taimakon
dakarun kasa da kasa da ke yaki da kungiyar.
An yi amannar cewa Boko Haram ta kama
dubbban mutane a shekaru taran da ta shafe
tana tayar da kayar baya, kuma ba wannan ne
karon farko da sojoji ke ikirarin kubutar da
jama’a ba.
Babu hotuna ko wata shaida da sojojin suka fitar
kawo yanzu, kuma babu bayani ko akwai ‘yan
matan makarantar nan ta Chibok da aka sace
shekara hudu da ta wuce a cikin wadanda aka
kwato din.
Wannan shi ne karo na uku a cikin wata hudu da
suka gabata da sojin ke ikirarin kwato mutane
daga hannun Boko Haram.
Jami’an tsaron Najeriya sun ce sun karya lagon
kungiyar amma har yanzu tana kai munanan
hare-hare musamman na kunar bakin-wake a
yankin arewa maso gabashin kasar.
Dubban mutane ne suka mutu a rikicin na Boko
Haram, yayin da sama da mutum miliyan biyu
suka rasa muhallansu.