A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari
zai bar Najeriya zuwa birnin London domin duba
lafiyarsa.
Wata sanarwa da babban mai taimakawa
shugaban kasa na musamman kan watsa labarai
Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Shugaba
Buhari zai shafe kwaki hudu likitocinsa suna
duba shi.
An fitar da sanarwar ne ranar Litinin da daddare,
kwana guda gabanin tafiyar shugaban zuwa
London.
Malam Garba Shehu ya ce ko a makon da ya
gabata ma Shugaba Buhari ya ga likitansa,
lokacin da jirginsa ya yi ratse a kan hanyarsa ta
komawa Najeriya bayan kammala ziyarar aiki a
Amurka.
Kakakin na shugaban kasa ya ce a lokacin ne,
likitan ya ce akwai bukatar sake duba lafiyarsa,
inda kuma shugaban ya amince.
Tuni dai aka dage ziyarar aiki ta kwanaki biyu da
aka tsara Buhari zai kai jihar Jigawa, inda yanzu
ake sa ran kai ziyarar bayan ya koma Najeriya
ranar Asabar, kamar yadda Garba Shehu ya
bayyana.
Yada zangon da Buhari ya yi a birnin London a
makon jiya ya janyo ce-ce-ku-ce da tambayoyi
daga ‘yan kasar da dama.
Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ma ta fitar da
sanarwa tana neman lallai a yi karin bayani kan
dalilin da ya sa Buhari zuwa London, duk kuwa
da hakan ba ya cikin tsarin tafiyarsa.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin
“hutun jinya”
5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar
dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman
bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman
majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga
gida”
28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar
Juma’a ba
3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman
majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a
a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin
jinya
25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan
sakon murya
11 ga watan Yuli – Najeriya Osinbajo ya gana da shi a
Landan
23 ga watan Yuli – Ya gana da wasu
gwamnoni
26 ga watan Yuli – Ya sake ganawa da wasu
karin gwamnoni
A bara Shugaban Najeriya ya shafe kusan wata
biyu yana jiya a birnin London, ta cutar da ba a
bayyanawa ‘yan kasar ainihin abinda ke damunsa
ba.
Batun rashin lafiyar shugaban ya janyo tsaiko
wajen tafi da al’amuran gwamnati da dama a
kasar.
Wasu ‘yan kasar sun yi ta zanga-zanga kan cewa
idan shugaban ba zai iya mulki ba to ya sauka,
ya mikawa mataimakinsa ragama.
A watan jiya ne Shugaba Biuhari ya bayyana
cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a
2019.