Al’ummar Musulmi a Jamhuriyar Nijar sun fara
azumin watan Ramadan ranar Laraba bayan
ganin jinjirin watan a wadansu yankuna na kasar
a ranar Talata.
Firai Ministan kasar Briji Raffini ne ya sanar da
ganin jinjirin watan azumin a wadansu yankuna
na kasar.
Sai dai ba a fara azumin ba a makwabciyar kasar
ba, wato Najeriya, saboda a ranar Laraba ne za a
fara neman jinjirin watan bayan Majalisar Koli ta
Addinin Musulunci ta bukaci hakan a farkon
makon nan.
Ita ma kasar Saudiyya za ta fara azumin ne a
ranar Alhamis bayan hukumomin kasar sun sanar
da cewa ba a ga watan ba a fadin kasar a ranar
Talata, wadda ta kasance 29 ga watan Sha’aban.
Hakazalika sauran kasashen Musulmin ciki har
da Indonisiya za a fara azumin ne a ranar
Alhamis.
Batun fara azumi da ajiye shi yana yawan jawo
ce-ce-ku-ce a kasashen duniya musamman a
Najeriya.
Ramadan dai wata ne da Musulmi suke
kauracewa ci da sha da kuma jima’i daga fitowar
alfijir zuwa faduwar rana, inda suke matsa kaimi
wurin ibada da addu’o’i.