Wannan ne hari mafi muni da aka kai a Pakistan tun shekarar 2014.
A cikin wadanda suka mutu akwai wani dan takara daga garin Mastung, kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka sanar. Kungiyar IS ce ta dauki alhakin kai harin.
Tun da farko, wani harin na daban da aka kai a garin Bannu ya janyo mutuwar mutum hudu.
Hare-haren sun auku ne gabanin zaben kasa da za a yi ranar 25 ga watan Yuli.
A wannan ranar ce aka kama tsohon firai minista Nawaz Sharif bayan da ya koma gida daga Ingila.
Hukumar NAB ce ta damke shi tare da ‘yar sa Maryam bayan sun sauka a birnin Lahore da ke arewacin kasar. Daga baya an wuce da su wani
gidan kurkuku a babban birnin kasar Islamabad.