BestArewaMusic | Northern Most Visited Entertainment Platform

Contact us For Music/Video Promotion Whatsapp: 09074457714, 07043434153 Email :bestarewamusic@gmail.com

Trending

Search BestArewaMusic

Saturday, 14 July 2018

Zaben Pakistan: Fiye da mutum 100 sun rasa rayukansu a harin bam

Wani dan kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 128 a lokacin wani gangamin zabe a kudu maso yammacin Pakistan.

Wannan ne hari mafi muni da aka kai a Pakistan tun shekarar 2014.

A cikin wadanda suka mutu akwai wani dan takara daga garin Mastung, kamar yadda jami'an 'yan sanda suka sanar. Kungiyar IS ce ta dauki alhakin kai harin.

Tun da farko, wani harin na daban da aka kai a garin Bannu ya janyo mutuwar mutum hudu.

Hare-haren sun auku ne gabanin zaben kasa da za a yi ranar 25 ga watan Yuli.

A wannan ranar ce aka kama tsohon firai minista Nawaz Sharif bayan da ya koma gida daga Ingila.

Hukumar NAB ce ta damke shi tare da 'yar sa Maryam bayan sun sauka a birnin Lahore da ke arewacin kasar. Daga baya an wuce da su wani
gidan kurkuku a babban birnin kasar Islamabad.

No comments:

Post a comment