• About
  • Contact Us
  • DMCA/Disclaimer
  • Privacy Policy
  • Sample Page
BestArewaMusic
No Result
View All Result
No Result
View All Result
BestArewaMusic
No Result
View All Result
  • Music
  • Videos
  • Hausa HipHop Music
  • News
  • International NEWS
  • Sports
Home News

Buhari ne ya bayar da umarnin cire Sarki Sanusi – Kwankwaso

AB Gentle by AB Gentle
March 11, 2020
in News
Reading Time: 6 mins read
2
42
SHARES
220
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dora alhakin tube Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu kan shugaba Muhammadu Buhari.

Jigon adawar, ya ce “shugabannin gwamnati na Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka ba su (su tube sarki Sanusi). Shi ya ba su umarni”.

Ya yi zargin cewa sabanin maganganun da makusantan Buhari ke cewa, shugaban ba ya tsoma baki cikin irin wadannan rigingimu, “sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani (Buhari) yana hargitsa inda yake sa hannu”.

“Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al’amuran jihar Kano”, in ji Kwankwaso. “Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu”.

Tun bayan daga aka cire sarki ranar litinin, gwamnatin Buhari a hukumance ba ta ce komai ba akan batun. Sai dai a makonnin baya Shugaba Buhari ya ce ba zai haka baki a harkokin cikin gida na jihar Kano ba.

Sai dai bestarewablog ba ta samu bayanai daga wasu kafofi masu zaman kansu ba da ke tabbatar da ikirarin Sanata Kwankwaso.

Kwankwaso, wanda a zamanin mulkinsa ne cikin shekara ta 2014 aka nada Sarki Muhammadu Sanusi II, yana wannan kalami ne lokacin zantawarsa da bestarewablog a kan batun cire tsohon sarki.

A ranar Litinin ne, gwamnatin jihar Kano ta sanar da tube rawanin basaraken, tare da korarsa daga Kano zuwa garin Awe cikin jihar Nasarawa, inda ake ci gaba da killace shi.

Tsohon gwamnan Kanon ya ce tube sarkin Kano, wani abin bakin ciki ne ga jihar Kano da Najeriya da ma duniya gaba daya, “dama shi mai martaba sarki, mutum ne na duniya gaba daya”.

A cewarsa daga abin da suka ji da abin da suka gani, ko shakka babu gwamnatin da ta san ya kamata ba za ta tube Muhammadu Sanusi ba.

Muhammadu Sanusi II, basarake ne mai yawan janyo ka-ce-na-ce kuma tun a lokacin mulkin Kwankwaso ya fara kai ruwa rana da gwamnatin jihar, har ta ba shi takardar gargadi karo biyu.

Sai dai Kwankwason ya musanta hakan, inda ya ce “ni ban taba ba Mai martaba sarki wata takardar gargadi ko ma wani abu irin wannan ba”.

Haka kuma an tambaye shi game da zargin da ake yi wa magoya bayansa ‘yan Kwankwasiyya wajen rura wutar rikici tsakanin Sarki Sanusi da Gwamna Ganduje, nan ma tsohon gwamnan ya ce su ba sa goyon bayan kowa sai bangaren gaskiya.

Ya ce a iyakar saninsa kamar yadda “su kansu mutanen gwamnati ke fada”, Sarki Sanusi ya gamu da fushin Ganduje ne saboda sun ce basaraken ya ce duk wanda ya ci zabe a Kano, a ba shi nasararsa.

Kwankwaso ya kuma koka kan abin da ya ce wulakancin da aka yi wa jama’ar jihar Kano ta hanyar wulakanta tsohon sarki.

Previous Post

BREAKING NEWS: ABU Zaria ASUU Secretriat Commence On Two Weeks Warning Strike – See Details t

Next Post

Governor El-Rufai appoints former Emir Sanusi chancellor of Kaduna State University

AB Gentle

AB Gentle

I Take Pictures Drink Chapman Eat And Sleep, CA Pro Graphics Designer, Cinematographer and A Blogger by Profession

Related Posts

Ty Rider - On Me x Misery

Ty Rider – On Me x Misery

by AB Gentle
March 22, 2023
0

...

Li Rye - Broken Heart

Li Rye – Broken Heart

by AB Gentle
March 22, 2023
0

...

femdot. - Pelle Pellet Ft. Sango

femdot. – Pelle Pelle Ft. Sango

by AB Gentle
March 22, 2023
0

...

Rvshvd - Ballin (Country Version)

Rvshvd – Ballin (Country Version)

by AB Gentle
March 22, 2023
0

...

Ajebo Hustlers - You Go Know Mp3 Download

Ajebo Hustlers – You Go Know Mp3 Download

by AB Gentle
March 22, 2023
0

...

Next Post

Governor El-Rufai appoints former Emir Sanusi chancellor of Kaduna State University

MUSIC: Hashim Zamah Neh – Abamu Dama Ft. Smokez X Tynking X Bash Neh Pha X Muda F

Comments 2

  1. Unknown says:
    3 years ago

    ???

    Reply
  2. Unknown says:
    3 years ago

    ???

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SEARCH BAM

No Result
View All Result

ADVERTISMENT

HOT ENTRIES

Ty Rider - On Me x Misery

Ty Rider – On Me x Misery

March 22, 2023
Li Rye - Broken Heart

Li Rye – Broken Heart

March 22, 2023
femdot. - Pelle Pellet Ft. Sango

femdot. – Pelle Pelle Ft. Sango

March 22, 2023
Rvshvd - Ballin (Country Version)

Rvshvd – Ballin (Country Version)

March 22, 2023
Ajebo Hustlers - You Go Know Mp3 Download

Ajebo Hustlers – You Go Know Mp3 Download

March 22, 2023
  • About
  • Contact Us
  • Privacy Policy
  • DMCA/Disclaimer

Copyright © 2016 - 2023 BestArewaMusic Inc.

No Result
View All Result
  • Music
  • Videos
  • Hausa HipHop Music
  • News
  • International NEWS
  • Sports

Copyright © 2016 - 2023 BestArewaMusic Inc.