Rashin Biyayya
Sarkin Kano yana nuna rashin biyayya ga umarnin ofishin gwamna da na sauran hukumomin gwamnati, ciki har da rashin halartar tarukan da gwamnati ke gayyatarsa ba tare da bayar da wata kwakkwarar hujja ba. Hakan rashin biyayya ne.
A bayyane take cewa sau da dama Malam Muhammadu Sanusi II ya ki yin biyayya ga sashe na uku karamin kashe na 13 (a – e) na dokar Masarautar Kano State ta shekarar 2019 kuma idan aka bar shi ya ci gaba da haka, zai bata mutuncin Masarautar Kano.
Kare Mutuncin Kano
Sanarwar ta kara da cewa an dauki matakin tube wa Sarki Sanisu II rawaninsa ne domin kare mutunci da al’ada da addini da kuma kimar Masarautar Kano wacce aka gina shekaru dubbai da suka gabata.
Sukar Manufofin Gwamnati
Mai sharhi a kan harkokin siyasa, Kabiru Sa’idu Sufi, Malam a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a da ke Kano, ya shiada wa BBC cewa babban dalilin cire Sarki Sanusi II daga kan mulki shi ne sukar da yake yi wa manufofin gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. ya bayyana cewa sukar da ya yi wa shirin gwamnatin jihar na karbo bashi daga kasar China domin gina layin dogo a cikin birnin Kano.
A matsayinsa na masanin tattalin arziki, Sarkin na Kano ya ce babu wani alfanu da za a samu idan aka ciyo bashi domin aikin babu wata riba da Kano za ta samu da shi.
Wannan kalami ya fusata gwamnatin Kano, abin da ya sa aka fara takun-saka, kuma dangantaka ta fara yin tsami.
Lamarin ya kai ga yunkurin sauke Sarki daga sarauta da kuma kaddamar da bincike kan zargin kashe kudin masarauta ba bisa ka’ida ba.
Wasu manya da suka hada da mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Alhaji Aliko Dangote sun shiga tsakani domin sasanta gwamnan Kano da Sarkin Kano.
Sai dai Sarkin ya sha cewa an jujyawa maganganunsa.
Siyasa
Magoya bayan gwamnatin jihar Kano sun sha kokawa kan zargin da suke yi wa sarkin na shiga harkokin siyasa.
Gwamnan Kano da magoya bayansa sun zargi Sarki Sanusi da goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna.
Sun yi zargin cewa ya fito fili ya yaki Ganduje, kuma ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP yakin neman zabe, sai dai sarkin ya musanta wannan zargi.
Wannan dalili ne ya sa lokacin da Gwamna Ganduje ya ci zabe karo na biyu, magoya bayansa suka shiga wani babban dakin taro na gwamnatin jihar suka cire hoton Sarki Sanusi II.
Hakan ya janyo gagarumar baraka tsakanin shugabannin biyu, lamarin da ya kai ga gwamnatin na yunkurin tube sarkin.
Kirkirar karin masarautu hudu a cikin Masarautar Kano ya yi matyukar harzuka masarauta da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Masarautun da Gwamna Ganduje ya kirkira su ne: Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano.
Hakan ya sa masu nada sari a kano gurfanar da gwamnatin Ganduje a gaban kotu lamarin da ya sake rura rikicin da ke tsakanin Sarki Sanusi II da Gwamna Ganduje.