Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai Salihu Tanko ya wallafa ta ce majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.
Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.
Karin bayani na nan tafe, amma kafin sannan ga abin da ya faru tun safiyar ranar.
Dama tun da safiyar Litinin Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Kanon kan yunkurin da majalisar ke yi na “ladabtar” da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne bayan bukatar da mataimakin shugabar majalisar dokokin, Hamish Ibrahim Chidari, ya yi cewa a gabatar da rahoton da kwamitin da majalisar ta kafa domin binciken Sarki Sanusi II.
Ranar hudu ga watan Maris ne majalisar ta ce ta karbi korafe-korafe biyu da suka zargi Sarki Sanusi II da yin kalaman da ba su dace da addinin Musulunci da al’ada ba.
Shugaban majalisar ya shaida wa ‘yan majalisa cewa ya karbi korafe-korafen ne daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al’ada ta Kano da kuma wani mutum, Muhammad Mukhtar mazaunin karamar hukumar Gwale.
Amma bai fayyace abubuwan da Sarki Sanusi II ya yi ba wadanda suka saba addini da al’adun Kano.
Daga nan ne shugaban majalisar ya bai wa kwamitin mako daya domin ya yi bincike sannan ya mika rahoton kan batun.