Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga mazauna jihar su yi azumi ranar Litinin domin rokon Allah Ya kawo karshen cutar coronavirus da ta addabi duniya.
Ko da yake ya zuwa ranar Litinin mutum 111 ne suka kamu da cutar a Najeriya, amma ba a samu bullar ta a Kano ba.
Hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta dauki matakai daban-daban wajen ganin coronavirus ba ta shiga jihar ba, ciki har da yin feshin magani a yankuna da lungunan jihar.
Ganduje ya yi kiran ne ranar Lahadi a yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum 38 da zai bayar da tallafi ga talakawa wadanda za su zauna a gidajensu a matakin dakile yaduwar cutar.
“Kazalika ina kira da al’ummar wannan jiha da su zage dantse wurin yin addu’o’i a masallatanmu a sallolin farilla biyar kowacce rana da kuma masallatan Juma’a domin ganin an dakile coronavirus daga jiharmu da kasarmu da ma duniya baki daya,” in ji Gwamna Ganduje.