Babban bankin Najeriya, CBN, ta ce wajibi ne bankunan kasar su mayar wa masu amfani da ATM kudi a cikin asusunsu nan-take idan kudin nasu ya makale.
Wannan umarni yana cikin sabbin ka`idoji da suka shafi makalewar da kudi ke yi yayin amfani da katin ATM da sauran hada-hada ta intanet da babban bankin ya gicciya wa bankunan.
Daraktan harkokin sadarwa na babban bankin Najeriya, Isaac Okorafor ne ya sanar da sabbin ka`idojin, wadanda ya ce sun fara aiki daga wannan wata na Yuni
Babban bankin ya ce idan kuma aka fuskanci wadansu matsaloli da suka shafi tangardar na`ura da sauran dangoginta, ya ba wa bankuna tsawon kwana guda domin jami`ansu su yi amfani da hannu su mayar wa mai kudin kudinsa a cikin asusunsa.
Dangane da wadanda kudinsu ya makale bayan sun yi amfani da katinsu na ATM a na`urar bankin da ba nasu ba kuwa, babban bankin ya umurci bankuna su cake wa mai kudi abinsu a cikin asusunsa cikin kwana biyu, sabanin yadda ake daukar tsawon kwana uku zuwa biyar a baya.
Babban bankin Najeriyar ya fitar da wadannan sabbin ka`idojin a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta ba wa bankuna damar budewa, tun bayan rufe su da aka yi sakamakon bullar annobar korona.
Kazalika CBN ya bayyana cewa ya gicciya ka`idojin ne da nufin kyautata hidimar da bankuna ke yi wa abokan huldarsu, tare da magance ko wane irin rinto.