Daya daga cikin jarumai mata acikin masana’antar Kannywood Aisha Najamu izzar so ta bayyana cewar bata ta’ammali da kayan maye kama daga kwaya kokuma wani abu wanda idan mutum yasha hankalinsa zai gushe domin ta aikata wani abu da akeso acikin film.
“Aisha Najamu izzar so ta bayyana cewar inda ace tanashan kwaya kokuma wani abun maye to bazata dingayin ayyukanta dakyau kamar yadda ake bukata daga wajan darakta, ta kara bayyana cewar indai har mutum yanshan kwaya ai bazai iya rike abind akeso ya fada ba”.
“Aisha Najamu takara bayyana cewar yanayin yadda takeyin (acting) acikin shirin wasan Hausa haka halittarta take, ahakan ma takara wasu abubuwa domin tabawa darakta abinda yakeson gani a tattare da ita”.
“Ta kara da cewar akwai wanda suke mata wani irin kallo, suna mata kallon wacce ba mutuniyar arziki ba, ta bayyana cewar ba haka takeba a gaske duk wani abu da’akaga tana aikatawa acikin film haka darakta yabata umarnin ta aikatashi amman a zahiri ba haka halinta yake ba”.
“Jarumar takara bayyana cewar ita mutum ce maison wasa da dariya akoda yaushe da mutane, haka zalika idan tana aiki tanaso darakta yadan bata lokaci domin tayi (chalikancinta) ita da sauran abokan wasanta awajan.”
Gadai cikakken bidiyon gamai bukatar kalla