Akalla Na Yiwa Maza Guda 80 Kaciya Bayyanar Mace Mai Yiwa Maza Kaciya Ya Janyo Cece-Kuce

0

Akalla Na Yiwa Maza Guda 80 Kaciya Bayyanar Mace Mai Yiwa Maza Kaciya Ya Janyo Cece-Kuce.

Mace Mai Yi Wa Maza Kaciya

Hassana Gambo Dakata kenan mai shekaru 17 a duniya, wadda ta gaji sana’ar wanzanci a wajen mahaifinta.

A cewar ta, kawo wa yanzu ta yi wa maza akalla guda tamanin kaciya.

Wannan labari shine ya janyo cece kuce a kafafen sada zumunta musammanma manhajar Facebook, inda akasamu gungun Mutane masu tofa albarkacin bakinsu. Ga kadan daga ciki;

Abdul Mb Jega yace:

“Allah Ka Shiryarta. Amma Ace Tayimin Kaciya DUK Yanda Zanyi Sai nayi Don Na Auri Yarta. Sauran Bayani Taji Ga Bakin Yarta.”

Real Suleiman yace:

“Kai Kaji Wani Sabon Iya Hege Do ALLah In dai Ba Sakarci ba Mai Zai kai ka Kaba Wannan Gogeggiyar Mata Kaciya Kawai Dai Itama Tana Iya Hegenta Ne Tana Rage ta Yaciin 🤣.”

Saman Na Ta’ala yace:

“Duk ranar da mijinta yabata mata rai tashin haushin maza duk yaron da yashiga hannunta a ranar gaba daya zata juya fushinta na maza akansa a kula fa 🥴.”

Rilwanu Ibrahim yace:

.”Wannan ba laifi ba ai, tunda likitoci maza suna karɓar haifuwar mata kuma suna tiyatar Gaban mata, Allah ya ƙara mata lafiya.”

Hajiya ummi tace:

“Lahaula Walaquwata 🙆🏻‍♀️.”

Yakubu yace:

“Mai yi wa yara maza dai ya kamata ku gyara rubutunku don har wasu sun fara yi mata mummunar fahimta suna zaginta wanda ba saba wa shari’a ta yi ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here