Gwannatin Buhari Ta Lalata Tattalin Arzikin Nijeriya Fiye Da Gwamnatin Jonathan, Cewar Sarki Sunusi II

0

Gwannatin Buhari Ta Lalata Tattalin Arzikin Nijeriya Fiye Da Gwamnatin Jonathan, Cewar Sarki Sunusi II.

DAGA Abubakar A Adam Babankyauta

Mai Martaba tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi na biyu ya bayyana damuwar sa kan halin da Nijeriya ke ciki, yana mai cewa, kasar ta tabarbare fiye da yadda take a zamanin Jonathan.

Sunusi Lamido Sunusi ya ce lokacin da shugaba Buhari ya karbi mulki daga hannun Jonathan tattalin arzikin Nijeriya bai tabarbare haka ba.

Sunusi na magana ne a wurin wani taro da Gidauniyar Akinjide Adeosun ta shirya kan sha’anin shugabanci a birnin Lagos da ke kudancin Nijeriya.

Sunusi Lamido Sunusi yace Nijeriya ce kasar da ke samar da man fetur amma take kokawa a halin yanzu a duniya bayan da farashin man ya tashi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.

Halin da Nijeriya ke ciki akarkashin wannan gwamnatin ya wuce tunanin mai tunani domin kudaden shigar mu bazasu iya biyan bashin da kasashen duniya ke bin mu ba, Inji Sunusi Lamido Sunusi.

Sunusi Lamido Sunusi ya saki ayar tambaya inda yake cewa, ta yaya tarihi zai tuna shugaban kasa da ministoci da gwamnonin da suka shafe tsawon shekaru 8 kan karagar mulkin Nijeriya amma suka gagara daura kasar akan tudun na tsari?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here