Innalillahi Amarya Ta Sumar Da Uwar Gida Wajen Rige Rigen Shiga Gaban Motar Miji a Kano

0

Innalillahi Amarya Ta Sumar Da Uwar Gida Wajen Rige Rigen Shiga Gaban Motar Miji a Kano.

Alkali ya aike da amarya gidan gyaran hali bayan da ta sumar da kishiyarta yayin da suke rige-rigen shiga gaban motar mijinsu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, lamarin ya auku a Kano ne a satin da ya wuce. Uwargida ta sanar da kotun shari’ar dake Kofar Kudun gidan Sarki a gaban Alkali Ibrahim Sarki Yola cewa, kishiyarta ta lakada mata duka.

Uwargidan dake kara tace bata cika lafiya ba, lamarin da yasa mijinsu ya aiko da mota a kai ta asibiti saboda ba za ta iya tuka motarta ba.

Uwargida ta bayyana cewa, tana shiga motar ne amarya ta rike kofa tana ce mata ta fito, inda ita kuwa tace ba za ta fito ba.

“Kafin kace wannan, sai na ji an make ni a goshi na. A take na fadi a sume kuma aka garzaya da ni asibiti,” cewar Uwargida.
A bangaren amarya kuwa, ta dire tace bata aikata hakan ba.

Mai shari’a Ibrahim Yola ya aike da amaryar gidan gyaran hali inda ya dage sauraron karar har zuwa sati na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here