Jami’an Tsaron Yankin Yarbawa Amotekun Sun Kama Wata Babbar Mota Makare Da Yan Arewa Dake Shirin Shiga Jihar Oyo

0

Jami’an Tsaron Yankin Yarbawa Amotekun Sun Kama Wata Babbar Mota Makare Da Yan Arewa Dake Shirin Shiga Jihar Oyo.

Jami’an Tsaro Na ‘Amotekun’ Dake Yankin Yarbawa Sun Kama Wata Babbar Mota Makare Da ‘Yan Arewa Dake Shirin Shiga Jihar Oyo Ci-Rani

Daga Muhammad Dahiru Shugaba

Tashar Talabijin ta TVC ta ruwaito cewa motar da ke kan hanyar zuwa Ogere a jihar Ogun daga Zamfara an tare ta ne a kusa da kasuwar Bodija da ke Ibadan bayan da wasu masu lura da al’amura suka yi ta kara kaimi tare da sanar da jami’an tsaro da abin ya shafa.

Kungiyar Amotekun na jihar Oyo ta yi gaggawar cimma matafiyan tare da kai moton matafiyan zuwa sansaninta, inda aka yi bincike sosai kan abinda matafiyan suka dauko, wanda daga ƙarshe suka gano cewa kayan abinci da jakunkuna na matafiyan ne kawai ke ciki motar.

Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Oyo kan Arewa Ahmed Murtala ya tabbatar da cewa mutanen matafiya ne kawai da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Ogun.

Ahmed wanda ya bayyana cewa za a mayar da matafiya zuwa jihohinsu ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da fifiko kan tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

Motar dai tana kan hanyar wucewa ne, wanda take dauke da maza dari da talatin da hudu da mata shida kamar yadda aka ce kimanin goma daga cikinsu sun tsere zuwa kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here